Mar 02, 2019 09:40 UTC
  • Yan Adawa A Kasar Algeria Sun Kara Da Jami'an Tsaro, Mutane 10 Suka Ji Rauni

Masu zanga-zangar nuna rashin amincewarsu da takarar shugaban kasar Algeria a zabubbuka masu zuwa sun kara da jami'an tsaro a kusa da fadar shugaban kasan.

Kamfanin dillancin labaran Irna na kasar Iran ya bayyana cewa jami'an tsaron kasar Algeria sun yi amfani da hayaki mai sa hawaye don tarwatsa masu zanga-zangar kin amincewa da sake shiga takarar shugaban kasa karo na 5 wanda shugaba Abdul-aziz Butaflika ya yi.

Mutane 10 ne suka ji rauni sanadiyyar karawar da jami'an tsaro suka yi da masu zanga-zanga.

Tun lokacin aka bayyana cewa shugaban dan shekara 81 a duniya, wanda kuma a zahiri bai da lafiya, zai sake shiga takarar shugaban kasa karu na 5 mutanen kasar Ageria , musamman matasa suka fara nuna amincewarsu da hakan. 

Shugaban Abdulaziz yana kan kujerar shugabancin kasar Algeria tun shekara 1999, sannan ya zuwa yanzu an zabe shi a matsayin shugaban kasar Algeria har sau 4. Amma a cikin hotunansa da ke bayyana a kafafen yada labarai baya ko iya tashi tsaye don tsofa da rashin lafiya. 

Za'a gudanar da zaben shugaban kasa a kasar Algeria a ranar 18 ga watan Afrilu na wannan shekara.

 

Tags