Mar 03, 2019 07:36 UTC
  • Dakarun Yemen Sun kai harin Daukar Fansa Kan Saudiyya

Sojoji da dakarun sa-kai na kasar Yemen sun kai hare-haren daukar fansa akan sojojin Saudiyya.

Rahotannin da suke fitowa daga kasar ta Yemen sun ce; Sojojin kasar sun harba makami mai linzami samfurin Zilzal-1 akan sansanin sojojin Saudiyya dake gundumar Asir a cikin kasar Saudiyya.

Kamfanin dillancin labarun “Tasnim” ya nakalto tashar talabijin din ‘al-masirah’ ta kasar Yemen na ba da labarin cewa; Sojoji da dakarun sa-kai na kasar ta Yemen sun harba makamin ne akan sansanin “Alab’ a gundumar ta Asir.

Harin da sojoji da kuma dakarun sa-kai na kasar Yemen suke kai wa Saudiyya yana zuwa ne a karkashin mayar da martani.

Tun a 2015 ne dai Saudiyya ta fara jagorantar kawance na yaki akan al’ummar Yemen wanda yake cigaba har yanzu. Adadin mutanen kasar da yakin na Saudiyya ya dauki rayukansu ya haura 13,000, yayin da wasu dubban dubata su ka jikkata.

Bugu da kari, hare-haren na Saudiyya sun lalata asibitoci da kuma cibiyoyin shan magani a fadin kasar ta Yemen.

 

Tags