Mar 04, 2019 12:44 UTC
  • Pakistan Ta Sanar Da Sake Bude Sararin Samaniyarta

Kasar Pakistan, ta sanar da sake bude sararin samaniyarta, data rufe sakamakon rikicin da ya kunno kai tsakaninta da India.

A cikin sanarwar data fitar hukumar kula da sufurin jiragen sama ta kasar, AAC, ta ce dukkan filayen sauka da tashin jigaren sama na kasar sun koma aiki.

A ranar Laraba data gabata ne, hukumar ta AAC, ta sanar da rufe sararin samaniyar kasar har sai abunda hali ya yi, bayan rikicin da ya kunno kai tsakanin kasshen makobtan juna, wanda ya kai ga kasarta Pakistan ta kakkabo jiragen yakin India guda biyu, a yayin da kuma ita Indiar ta sanar harbo wani jirgin yakin Pakistan guda.

Tsohuwar gaba tsakanin kasashen biyu ta sake zafafa ne a karshen watan Jiya, bayan da jiragen yakin India, suka kai farmaki kan yankin Kashmir na bangaren Pakistan da ke kan iyakarsu, inda Indian ta ce sansani ne na ‘yan ta’adda da ke shirin kaddamar da hare-hare akanta.

India ta kai farmakin ne makwanni kalilan, bayan da a farkon watan na Fabarairu kungiyar da ke kiran kanta da J.E.M. ta dauki alhakin harin kunar bakin waken da ya hallaka sojin India 40, a yankin na Kashmir.

Tags