Mar 05, 2019 13:51 UTC
  • PLO Ta Yi Allawadai Da Amurka Game Da Rufe Ofishinta A Jerusalem

Kungiyar (PLO), mai fafutukar kwato 'yancin Palastinawa ta yi Allawadai da matakin Amurka na rufe karamin ofishin jakadancinta dake Jerusalem.

Kwamitin kungiyar ta PLO, ne ya sanar da hakan, bayan matakin Amurka na rufe ofishin da kuma hade shi da na Israi'la.

"Rufe karamin ofishin jakadancin Amurka a Jerusalem da kuma hade shi da ofishin jakadancinta dake Isra'ila ya kasance a matsayin saba yarjejeniyar kasa da kasa wanda ita da kanta Amurkar ce ta jagoranci tsara daftarin yarjejeniyar," inji kungiyar ta PLO.

Game da batun rufe karamin ofishin jakadancin da Amurkar ta yi, PLO ta kuma yanke shawarar ci gaba da daukar matakai na katse duk wata huldar siyasa tsakaninta da kasar Amurka.

Tags