Mar 06, 2019 09:24 UTC
  • Jakadan Brazil A Siriya Ya Koma Bakin Aikinsa A Birnin Damascas.

Jakadan kasar Brazil a kasar Siriya ya koma bakin aikinsa bayan shekaru kimani 7 da barin kasar.

Kamfanin dillancin labaran gwamnatin kasar Siriya SANA ya bayyana cewa Jakadan kasar Brazil a kasar Siriya ya mika takardun komawa bakin aikinsa ga ministan harkokin wajen kasar Siriya Walidul Mu'allim.

Labarin ya kara da cewa Fabiu-Fas Bitoluca ya bar birnin Damascas ne a shekara 2012 saboda matsalolin tsaro, amma duk tare da haka kasar Brazil ta bar karamin ofishin jakadancin kasar tana aiki a birnin Damascus a duk tsawon wannan lokaci.

A wannan karon dai jakadan kasar ta Brazil a Siriya ya ce gwamnatinsa tana son zuba jari a shirin gwamnatin kasar na sake gina kasar. 

Kafin haka dai ita ma gwamnatin kasar ta siriya ta bukaci sake dawo da huldan tattalin arziki na kasar ta Brazil a cikin watan Jenerun shekra ta 2018 da ta gabata.

Ya zuwa yanzu dai mafi yawan kasashen Larabawa da kuma kasashen Turai sun sake bude ofisoshin jakadancinsu a birnin Damascas, bayan an sami zaman lafiya a birnin da ma mafi yawan yankunan kasar.

Tags