Mar 15, 2019 08:25 UTC
  • Sama Da Mutum 370,000 Suka Mutu A Yakin Siriya (OSDH)

Hukumar dake sa ido kan al'amuran kare hakkin bil adama a Siriya ta fitar da wani rahoto dake cewa, sama da mutum 370,000 ne suka rasa rayukansu tun bayan yakin da ya barke a cikin shekara 2011 a kasar Siriya.

Wannan dai na zuwa ne a daidai lokacin da aka shiga shekara tara cif da yakin na Siriya.

Rahoton na kungiyar ta OSDH ya ce daga cikin mutanen 112,623 fararen hula ne, da suka hada da yara sama da 21,000 da kuma mata 13,000.

Rikicin Siriya ya rikide zuwa yakin basasa ne, bayan da mayakan dake ikirari da sunan jihadi da 'yan tawayen dake samun goyan bayan wasu kasashenyankin da kuma dakarun kasashen ketare suka sanya hannu a yakin.

Tags