Mar 17, 2019 16:00 UTC
  • Pakistan : Harin Bam Ya Yi Ajalin Mutum 4

Rahotanni daga Pakistan na cewa akalla mutum hudu ne suka rasa rayukansu a wani harin bam da aka kai kan jirgin kasa a kudu maso yammcin kasar.

'Yan sanda a kasar sun ce an tada bam din ne daga nesa, a daidai lokacin da jirgin kasa ke wucewa lamarin da yayi sanadin mutuwar mutum hudu da kuma raunata wasu bakwai na daban.

Harin dai ya wakana ne a yankin Baloutchistan, dake raba da iyakar kasashen Afganistan da kuma Iran.

Shugaban 'yan sandan yankin, Irfan Bashir, ya shaidawa kamfanin dilancin labaren AFP cewa, jirgin kasa ya tashi ne daga lardin Quetta zuwa Rawalpindi, a lokacinda ya taka bam din da aka sarrafa daga nesa.

Har lokacin zuwa karanto wadanan labaren babu wata kungiya data dau alhakin kai harin.