Mar 19, 2019 06:21 UTC
  • Manyan Hafsoshin Sojin kasashen Iran, Iraki, Syria, Sun Gana A Kasar Syria

Manyan hafsoshin sojin kasashen Iran, Iraki da Syria, sun gudanar da wata ganawa a birnin Damascus na kasar Syria.

Kamfanin dillancin labaran SANA ya bayar da rahoton cewa, a yayin ganarwar da suka gudanara  jiya, manyan hafsohsin sojin kasashen Iran janar Muhammad Baqiri, da na Iraki janar Usman Al-ganimi, da kuma na Syria Janar Ali Abdullah Ayyub, sun tattauna muhimman batutuwa da suka shafi ayyuka na tsaro an hadin gwiwa a tsakanin rundunonin sojojin kasashen uku.

Babban hafsan hafoshin sojin kasar Syria Janar Abdullah Ayyub ya bayyana cewa, a halin yanzu kasashen uku sun zama tsintsiya daya madaurinki daya, kuma sun kafa kawance na gudanar da ayyukan tabbatar da tsaro a tsakaninsu.

Bayan kammala ganawar, dukkanin manyan hafsoshin sojin kasashen uku sun gana da shugaba Bashar Assad na kasar ta Syria, inda ya jadda cewa babu gudu abbu ja da baya wajen yaki da ayyukan ta’addanci da wadanna kasashe suka sanya  a gaba, ya kuma jinjinawa kasashen Iran da Iraki kan irin gagarumar gudunmawar ad suka baiwa Syria a dukaknin bangarori, inda ya ce alaka a tasakanin wadannan kasashe uku ta tarihi ce.