Mar 19, 2019 09:39 UTC
  • An Hallaka Sojojin Hayar Saudiya 15 A Lardin Najran

Cikin wani farmakin mayar da martani da Sojoji gami da Dakarun sa kai na kasar Yemen suka kai yankin Mustahdis na Lardin Najran dake kudancin Saudiya sun samu nasarar hallaka Sojojin saudiya 3 da Sojojin haya 12.

Tashar talabijin din Al-masira ta kasar Yemen ta habarta cewa a wannan Talata Sojoji da dakarun sa kai na kasar sun hallaka sojojin hayar saudiya 15 a lardin Najran dake kudancin kasar Saudiya.

Ko baya ga hakan, dakarun sa kai na kasar Yemen din sun kai hari kan matattarar Sojojin hayar saudiya a yankin Sudais dake lardin Najran, a yayin wannan harin, Dakarun tsaro na Yemen sun samu nasarar hallaka wani adadi mai yawa na Sojojin hayar Saudiyan tare da mamaye sansanin nasu.

Har ila yau, Sojojin Yemen din sun  tarwatsa wata motar sojin hayar saudiya a filin sahara na Al-Buku'u dake lardin na Najran, tare da hallaka dukkanin mazauna motar.

Abin tuni dai a nan tun a watan Maris din shekarar 2015 ne, kasar Saudiya da hadaddiyar daular Larabawa bisa cikekken goyon bayan Amurka suka kaddamar da harin wuce gona da iri kan al'ummar kasar Yemen tare da killace kasar ta sama, kasa da kuma ruwa, lamarin da ya yi sanadiyar mutuwar Yamaniyawa sama da dubu 16 da kuma raba wasu milyoyi da mahalinsu, bisa kididdigar Majalisar Dinkin Duniya

A yayin da yakin ya shiga cikin shekaru na 4 har ya zuwa yanzu kasar Saudiyar tare da kawayenta sun kasa cimma manufofinsu a kasar ta Yemen, saboda  juriya da gwagwarmayar al'ummar ta yemen  na kare kasarsu.