Oct 07, 2016 18:25 UTC
  • Shugaban Colombia Juan Manuel Santos Ya Lashe Kyautar Nobel Na Zaman Lafiya

An sanar da shugaban kasar Colombia Juan Manuel Santos a matsayin wanda ya lashe kyautar Nobel ta zaman lafiya na shekara ta 2016 sakamakon kokarinsa wajen cimma yarjejeniyar sulhu da 'yan tawayen Farc na kasar duk kuwa da rudanin da ke tattare da yarjejeniyar a halin yanzu.

Rahotanni sun ce alkalan da ke zaba a kasar Norway sun sanar da sun sanar da shugaban kasar Colombia Juan Manuel Santos a matsayin wanda ya lashe kyautar ta Nobel ta bana (2016) saboda kokarin da ya yi wajen kawo karshen yakin basasan kasar da aka shafe sama da shekaru 50 ana yinsa ta hanyar kulla yarjejeniyar sulhu da kungiyar Farc ta 'yan tawaye.

A kwanakin baya ne dai shugaba Santos din ya kulla yarjejeniyar sulhu da jagoran kungiyar Farc din lamarin da kasashen duniya da dama suka yaba, to sai dai al'ummar kasar sun yi watsi da haka a  zaben raba-gardamar da aka gudanar a makon da ya wuce a kasar.

Kididdiga dai  a ce alal akalla mutane 260,000 ne suka rasa rayukansu, wasu dubu 45 kuma sun bace kamar yadda wasu kimanin miliyan 7 sun rasa matsugunansu sakamakon yakin basasar da aka shafe shekaru 52 ana yi  a kasar.

 

Tags