Apr 08, 2017 12:07 UTC
  • Amurkawa Sun Yi Zanga-Zangar Kin Amincewa Da Kai Wa Kasar Syria Hari

Dubban Amurkawa sun yi gangami da zanga-zangar yin Allawadai da ta salon siyasar ina da yaki da Donald Trump wadda ta kai shi ga kaddamar da hari a kan kasar Syria saboda dalilai na siyasa.

Tashar talabijin ta Press TV daga birnin New York ta bayar da rahoton cewa, an gudanar da wannan jerin gwano a birane daban-daban na kasar Amurka, da suka hada da Washington, New York, Los Angeles, Filadelfia da sauransu.

Masu zanga-zangar sun karba kiran kungiyoyin farar hula ne masu adawa da siyasar yaki irin ta gwamnatin Amurka, inda a birnin New York Amurkawa da dama suka yi cincirindo a gaban babban ginin Trump Power mallakin shugaban kasar ta Amurka, inda suke la'antar siyasarsa, tare da yin tir da Allawadai da harin da ya kaddamar a kan kasar Syria, inda suke cewa ba da sunansu ba.

Wasu daga cikin 'yan majalisar dokokin Amurka sun bukaci da aikewa Trump da ya bayyana a gaban majaliasr domin ya yi mata karin bayani kan dalilain kai hari Syria ba tare da izinin majalisa ba.

Tags