May 31, 2018 06:44 UTC
  • Kashi 50% Na Kananen Yarar Duniya Na Fuskantar Barazanar Yaki Da Yunwa.

Wata Kungiyar ceton yaran Duniya ta kasar Birtaniya ta bayar da rahoton cewa kashi 50% na yara a Duniya na fuskantar barazana daga yaki, tsananin talauci da kuma bambanci.

Kamfanin dillancin labaran kasar Faransa ta nakalto kungiyar Save the Children ta kasar Birtaniya cikin wani rahoto da ta fitar mai taken fuskoki mabambanta na wariya da ya tattaro rahoto daga kasashe 175 kan matsalar da yara kimanin bilyan daya da miliyan 200 ke fuskanta a Duniya.

Rahoton ya ce 'yan mata miliyan 575 dake rayuwa a duniya na fuskantar wariya kuma wannan matsala ce babba.

Rahoton ya ce duk da cewa kasashen Amurka, Rasha da China nada karfin tattalin arziki, tsaro da kuma fusaha, amma suna daga cikin jerin kasashen da yara ke fuskantar irin wadannan matsaloli.

Kungiyar ta bukaci daukan mataki domin kawo karshen matsalar da yara ke fuskanta a Duniya.

Tags