Jul 01, 2018 15:59 UTC
  • Indiya : Hatsarin Motar Bus Ya Yi Ajalin Mutum 48

A Indiya mutane a kalla 48 ne suka rasa rayukansu a wani hatsarin motar bus a aynkin himalaya na Uttarakhand dake arewacin kasar.

Ko baya ga wadanda suka rasa rayukansu da akwai wasu 13 da suka raunana, ciki har wadanda suka ji munanen raunuka.

Bayanai sun ce motar bus din shake da mutane ta kwace wa dreban ne, ta fita hanya ta fada cen kusa da wani kogi ta dare gida biyu.

Kantoman lardin  Sushil Kumar, ya shaida wa masu aiko da rahotannin cewa, mutane 61 ne ke cikin motar bus din, wacce akayi ta don daukar mutum 28, wannan yake nuna cewa wuce kima yawan mutane da motar ya kamata ta dauka ya taimaka wajen samun hasara rayuka masu yawa.

Wannan hatsarin dai na daga cikin mafi muni da suka auku baya baya nan a wannan yankin, baya ga wani wanda ya yi sanadin mutuwar yara 'yan makaranta 30 a  lardin Himachal Pradesh.

A Indiya dai kiyatsi ya nuna cewa mutane 150,000 ne rasa rayukansu sanadin hatsuran mota a cikin shekara.

 

Tags