Jul 04, 2018 06:46 UTC
  • Yan Sanda A Kasar Birtaniya Sun Kama Wata Ma'aikaciyar Jinya Kan Zargin Kashe Jarirai

Rundunar 'yan sandan Birtaniya ta sanar da kame wata ma'aikaciyar jinya kan zargin hannu a kashe jarirai takwas a wani asibitin kasar.

Kamfanin dillancin labaran Reuters ya habarta cewa: Rundunar 'yan sandan Birtaniya ta kame wata ma'aikaciyar jinya a wani asibiti da ke shiyar arewa maso yammacin kasar a jiya Talata kan zargin hannu a kashe jarirai takwas tare da kokarin halaka wasu shida na daban.

Fitar da rahoto kan yawan mutuwar jarirai a wannan asibiti ne ya ja hankalin mahukuntan lafiya a kasar lamarin da ya sanya aka mika rahoton ga rundunar 'yan sandan Birtaniya domin gudanar da bincike, inda bincike ya kai ga kame wannan ma'aikaciyar jinya da ake zargi da hannu a kashe jariran.

Tags