Jul 08, 2018 17:07 UTC
  • Thailand : An Ceto 6 Daga Cikin Yaran Da Suka Makale A Kogo

A Tailand, An yi nasarar fito da shida daga cikin yaran da suka makale a wani kogo dake arewacin kasar, makwanni biyu da suka gabata.

Bayanai sun ce sai nan zuwa gobe Litini za'a ci gaba da aikin ceton, domin fitar da sauren yaran, kasancewar aikin yana da hatsarin gaske, don kada ruwa su kara cika kogon.

Daga kafin hakan masu aikin ceton sun shaida cewa aikin fito da yaran zai dauki kusan kwana uku ana yi, duk da cewa babu tabas akan hakan, kasancewar za'a dinga fito da yaran ne daya bayan daya.

Da safiyar yau Lahadi ne aka fara aikin fito da yaran su 12, wadanda dukkaninsu maza ne tare da kocinsu na kwallon kafa, kusan mako 2 ke nan da suka makale a kogo sakamakon wata ambaliyar ruwa da aka yi.

Ma'aikata fiye da dubu ne da suka hada da kwararu akan ninkaya, wadanda suka fito daga kasashen China da Myanmar Australia da Amurka da kuma Birtaniya, da Laos suka shiga aikin ceton.

Tags