Jul 10, 2018 17:18 UTC
  • Za A Kafa Dokar Hukunta Shugabannin Addinin Buda Masu Karbar Rashawa A Thailand

Majalisar dokokin kasar Thailand ta kada kuri'ar amincewa da daftarin dokar hukunta jagororin addinin buda masu barnata dukiyar kasa.

A zaman da majaisar dokokin kasar ta Thailand ta gudanar a jiya, ta kada kuri'ar amincewa da daftarin dokar hukunta jagororin addinin buda masu barnata dukiyar al'umma.

Jagororin addinin buda a kasar Thailand dai suna da matsayi na musamman, inda wasu daga cikinsu suke yin amfani da wannan damar cin karensu babu babbaka kan dukiyar kasar da sunan addini.

Dukkanin 'yan majalisar dokokin kasar su 217 ne suka amince da wannan daftarin doka, wanda zai bayar da damar hukunta jagororin addinin na buda kasar, wadanda ake kallon a matsayin suna a birbishin doka.

Tags