Aug 02, 2018 18:51 UTC
  • A Kame Wani Tsohon Ministan Masar A Italiya

Jaridar al-quds al-arabi ta kawo labarin cewa jami'an tsaron kasar Italiya sun kame Muhammad Mahsub wanda tsohon minista ne a kasar Masar.

Muhammad Mahsub ya rubuta a shafinsa na Twitter cewa; Jami'an tsaron kasar ta Italiya sun kama shi ne a garin Katania bisa bukatar mahukuntan kasar Masar., Mahsub ya ci gaba da cewa; kawo ya zuwa yanzu babu wata tuhuma da 'yan sandan su ka yi masa.

Mahsub ya rike mukamin ministan shari'a ne a lokacin gwamnatin Muhammadu Mursi, kamar kuma yadda ya rike wasu mukamai a majalisar dokokin kasar ta Masa.

A shekarar 2015 wata kotu a kasar Masar ta yanke masa hukuncin bayan fage na zaman kurkuku tsawon shekaru uku. A shekarar 2016 gwamnatin Masar ta mika sunansa ga hukumar 'yan sandan duniya akan su kamo mata shi.

Tags