Aug 05, 2018 18:55 UTC
  • Iran Ta Yi Allah Wadai Da Yunkurin Kisan Shugaban Kasar Venezuela.

Kakakin ma'aikatar harkokin wajen kasar Iran ya yi allawadai da yunkurin kashe shugaban kasar Venezuela da aka yi a yau Lahadi.

Bahram Qasimi ya kara da cewa kokarin kashe shugaban kasar Venezuela Nicolas Madoro wani aikin ta'addancin ne kuma manufar haka shi ne rikita kasar da kuma taimakawa makiyan kasar. 

A safiyar yau lahadi ne wani abu ya fashe a lokacinda shugaban kasar ta Venezuela yake jawabi a wani taro da sojojin kasar a birnin Karakas babban birnin kasar.

A lokacin kai harin dai gidan talabijin ta kasar Venezuela tana yada jawabin shugaban kasar kai tsaye. 

Daga baya shugaban ya zargi gwamnatin kasar Colombia da hannu wajen taimakwa yan tawayen kasar wadanda suka kai harin na yau. Sannan an kama wasu mutanen da ake tuhuma da hannun cikin kokarin kashe shugaban kasar ta Venezuela.

 

Tags