Aug 10, 2018 18:56 UTC
  • Hukumar Kula Da Makamashi ta Duniya Ta Yi Gargadi Kan Sanya Takunkumin Man Fetir A Kan Iran

Cikin wani sabon rahoto da ta fitar Hukumar kula da Makamashi ta Duniya, IEA,ta ce takukumin da Amurka ta kakabawa Iran na sayar da man fetir, idan ya fara aiki zai dagula kasuwar man fetir a Duniya

A rahoton da take fitarwa ko wani wata, a yau juma'a Hukumar kula da Makamashi ta Duniya, IEA, ta ce matakin da Amurka ta dauka na kakabawa Iran takumkumi kan man fetir, zai iya tasiri a kasuwar man fetir ta Duniya, kuma zai sanya kasashen da suke fitar da man fetir cikin matsi na cike gurbin Man da kasar Iran din  ke samarwa.

Rahoton  ya ce idan har wannan takunkumi ya fara aiki, kasuwar dan man fetir za ta fuskanci kalu bale, da hakan kuma na iya man fetir din ya yi tashin kwabron zabi a Duniya.

Wannan rahoto na Hukumar kula da Makamashi ta Duniya, na zuwa ne a yayin da wasu takunkumin da Amurka ta kakabawa kasar Iran ya fara aiki tun a ranar 7 ga watan Augustan da ta gabata, sannan kuma a farkon watan Nuwamba mai zuwa, takunkumin sayar da man fetir din zai fara aiki.

Duk da cewa dai kasar Amurkan ta yi barazanar kakaba takunkumi kan duk wata kasa da ta ci gaba da sayar Man na Iran daga farkon watan Nuwamba, to amma kasashen China da Indiya dake a matsayin manyan kasashen da suke sayan man na Iran sun ce ba za su umarnin Amurkan ba.

Tags