Aug 21, 2018 18:59 UTC
  • MDD Ta Yi Allah Wadai Kan Harin Da Kungiyar Boko Haram Ta Kai A Najeriya

Babban Saktaren MDD ya yi Allah wadai kan harin ta'addancin da kungiyar Boko haram ta kai a arewa maso gabashin Najeriya

Cikin wata sanarwa da ya fitar a wannan Talata, babban saktare janar na MDD  ya yi Allah wadai kan harin ta'addancin da mayakan Boko Haram suka arewa maso gabashin Najeriya, sannan ya bukaci a gaggauta gudanar da bincike tare da gano maharan da kuma gurfanar da su a gaban kuliya.

Cikin bayanin nasa António Guterres ya nuna tsananin takaicinsa kan yadda rikici ke kara kamari a yankin tabkin Tchadi, sannan ya bukaci kungiyar Tarayyar Afirka da tayi kokarin tabbatar da sulhu da tsaro a yankunan da ake rikici a kasashen Afirkan.

Har ila yau babban saktaren MDD ya bukaci kungiyoyin kasa da kasa da suka taimakawa rundunar yankin tabkin Tchadi dake yaki da kungiyar Boko haram.

A Daren lahadin da ta gabata ce mayakan boko haram suka kai farmaki a wasu gariruwa  na arewa maso gabashin Najeriya inda suka kashe fararen hula da dama tare kuma da kone kauyuka da dama a yankin.

Tags