Sep 12, 2018 11:53 UTC
  • Bolivia Ta Yi Allawadai Da Tsawaita Takunkuman Da Amurka Ta Dorawa Kasar Cuba.

Shugaban kasar Bolivia Evo Marales ya yi Allawadai da tsawaita takunkuman kasuwanci wanda gwamnatin Amurka da dorawa kasar Cuba.

Kamfanin dillancin labaran "Pranslatino" ta kasar Cuba ta nakalto shugaban yana fadin haka a cikin shafinsa na Tweeter, ya kuma kara da cewa gwamnatin kasar Amurka tana son dukkan kasashen duniya su zama mafi biyaya ga umurninta, amma mutanen cuba ba za su taba mika kai ba.

A ranar Talata ce gwamnatin shugaba Donal Trump ta tsawaita takunkuman kasuwanci kan kasar Cuba na tsawon shekara guda.

Wani abin lura a nan shi ne gwamnatin Amurka ta fara dorawa kasar Cuba takunkuman tattalin arziki ne tun shekara 1962 wato a zamanin shugaba John F Kennedy  

Tags