Sep 22, 2018 17:45 UTC
  • China Ta Gayyaci Jakadan Amurka Kan Kakaba Mata Takunkumi

Ma'aikatar harkokin wajen China, ta kirayi jakadan AMurka a birnin Pekin, domin bayyana masa fishin kasar akan takunkumin da Amurkar ta kakaba wa wani bengaren sojin kasar, saboda sayen makaman yakin Rasha.

A ranar Alhamis data gabata ne mahukuntan Washington, suka sanar da kakaba wa China takunkumi saboda sayen jiragen yaki da makamai masu linzami na Rasha.

Kafin hakan dama a ranar Juma'a data gabata, mahukuntan na Pekin sun bukaci Amurka data janye wannan takunkumin ko kuma ta jira abunda zai biyo baya.

Kakakin ma'aikatar harkokin wajen China, Geng Shuang, ya ce wannan matakin na Amurka ya matukar sabawa huldar kasa da kasa, sannan barazana ne ga huldar dake tsakanin sojojin kasashen biyu.

Wanann dai na zuwa ne a daidai lokacin da, mahukuntan Moscow, da huldar dake tsakaninta da Amurka ta fuskanci koma baya, ke zargin Amurka da yiwa zaman lafiya duniya barazana.

Tags