Sep 25, 2018 16:29 UTC
  • MSF Ta yi Gargadi Akan Yawan Mace Macen Yara A Nijar

Kungiyar likitoci marar iyaka ta (Médecins sans frontières), ta yi gargadi akan yawan mace macen yara 'yan kasa da shekara 5 a Kudancin Jamhuriya Nijar.

A rahoton data fitar kungiyar ta MSF, ta ce yara kimanin goma ne ke rasa rayukansu a ko wacce ranar ta Allah, a garin Magaria dake kudancin kasar ta Nijar.

Rahoton ya ce yara na fama ne da matsananciyar cutar malaria ko zazzabin cizon sauro, da kuma tamowa ko matsalar karamcin abinci mai gina jiki.

Yau sama da wata guda kenan da tawagar kungiyar ta MSF, dake kula da lafiyar yara ke yaki da mace macen yara 'yan kasa da shekara 5 a garin Magaria.

Kungiyar ta ce tare da hadin gwiwar hukumomin kiwan lafiya na kasar ta Nijar, yanzu haka tana kula da yara 730 a cibiyarta dake Magaria, wandanda 208 daga cikinsu ke cikin mawuyacin hali.

Tags