Oct 04, 2018 18:01 UTC
  • Rasha : Putin Ya Fara Ziyara A Indiya

Shugaba Vladimir Putin na Rasha, ya fara wata ziyarar aiki ta kwanaki biyu a birnin New Delhi na kasar Indiya.

A yayin ziyarar shugaba Putin, zai gana da kuma yin liyafar abibnci tare da fira ministan kasar ta Indiya, Narendra Modi. 

Babban batun da bangarorin zasu tattauna shi ne kammala cinikin makamman kariya na hare hare sama samfarin S-400 da Indiya ta saya ga Rasha, wanda ya kai sabar kudi Dalar Amurka kimanin Biliyan biyar.

Kasashen Indiya da Rasha dai nada kyakyawar dangantaka musamman kan cinikayya ta kayan tsaro.

Saidai babban kalubalen dake tattare da cinikin shi ne barazanar da Amurka ta yi na kakaba takunkumin tattalin arziki ga duk wata kasa data sayi makamai kirar Rasha.

Tags