Oct 11, 2018 07:47 UTC

Wasu kafofin yada labaran kasar Turkiya sun samu wasu hotunan bidiyo daga hannun jami'an tsaron kasar, da suke nuna yadda jami'an tsaron Saudiyya suka shiga karamin ofishin jakadancin Saudiyya a Istanbul, bayan shigar Jamal Khashoggi a cikin wurin.

Tashar talabijin ta Aljazeera ta bayar da rahoton cewa, hotunnan bidiyon wadanda aka samu daga hannun jami'an tsaron Turkiya masu gudanar da bincike, sun nuna yadda wasu jami'an tsaron Saudiyya 15 suka iso kasar a ranar Talata 2 ga wannan wata na Oktoba, ranar da aka bukaci Khashoggi ya dawo ofishin domin karbar wasu takardu.

Haka nan kuma hotunan sun nuna shigar Khashoggi, jim kadan kuma jami'an tsaron suka iso wurin,bayan kimanin sa'oi biyu jami'an tsaron na Saudiyya sun fito daga ofishin, amma Khashoggi bai fito ba har inda yau take.

Saudiyyah dai tana bayyana cewa ba ta san makomarsa, yayin da jami'an tsaron kasar Turkiya suke ci gaba da gudanar da bincike, wanda za su sanar da sakamakonsa a nan gaba.

Tags