Oct 14, 2018 12:09 UTC
  • Aiki Tare Tsakanin Rasha Da Iran Zai Rage Tasirin Takumkumin  Amurka.

Wani jami'in kasar Rasha ya ce aikin tare tsakanin kasashen Rasha da Iran zai rage tasirin takunkumin da kasar Amurka ta kakabawa kasashen biyu.

A yayin da yake fira da kamfanin dillancin labaran Irna Ismael Sha'aban Uf gungu a majalisar kula da kabilun kasar Rasha ya ce a halin da ake ciki, wajibi ne kasashen Rasha da Iran su kara gina alakar dake tsakaninsu wanda kuma hakan zai rage tasirin takunkumin da Amurka gami da kawayenta suka kakabawa kasashen biyu.

Sha'aban Uf  ya kara da cewa kasashen Iran da Rasha na taka mahimiyar rawa a bangare masana'antu, ci gaban ilimi da harakokin Noma gami da kasuwanci a Duniya, wannan kuma babban makami ne na kalubalantar takunkumin zalincin da kasar Amurka ta kakabawa kasashen biyu.

Yayin da yake ishara kan rage tasirin Amurka a Duniya, Sha'aban Uf  ya ce kungiyar tarayyar Turai ta fara raba gari da kasar Amurka, kuma kasashen Duniya za su fahimci tsarin zalinci na kasar Amurka.

Tags