Oct 26, 2018 11:45 UTC
  • An Sake Bankado Hannun Dakarun Faransa A kisan Kiyashin Rwanda

An fityar da wani hoton bidiyo dake nuna cewa sojojin Faransa nada labarin kisan kiyashin da ya faru a Ruwanda a shakarar 1994.

Shaffin bincike na Mediapart, ce ta fitar da wani hoton bidiyo da ke nuna babban hafsan rundunar sojin Faransa Kanal Jacques Rosier, na zantawa da wani karamin soji da ke karkashinsa na sanar da shi cewa sun ziyarci wani yanki da aka aiwatar da kisan kiyashin kasar Rwanda a waccen lokacin.

Labarin kuma ya kara da cewa akwai yiyuwar sojojin Faransar sun yi mu'amulla da wani wanda ya jagoranci kisan kiyashin na kabilar Hutu.

Rundinar sojin Faransa dai ta jima tana musanta cewa tana da masaniya akan abunda ya faru a yankin na Bisesero a watan Yuni na 1994.

Tags