Oct 27, 2018 15:46 UTC
  • Kasashen Rasha, Jamus, Faransa Da Turkiyya Na Taro Kan Siriya

Shugabannin kasashen Rasha, Faransa, Turkiyya da kuma Jamus na wani taro a birnin Santanbul kan batun Siriya.

Taron wanda shi ne irinsa na farko na maida hankali ne kan yadda za'a karfafa yarjejeniyar tsagaita wuta a yankin Idleb da kuma duba hanyoyin samar da wani canji na siyasa a kasar ta Siriya.

An shirya dai za'a yi ganawa tsakanin shugabannin da suka hada da Recep Tayyip Erdogan na Turkiyya da Vladimir Putin na Rasha da Emmanuel Macron na Faransa da kuma shugabar gwamnatin Jamus Angela Merkel.

Ko baya ga wadanan shugabannin da akwai wakilin Majalisar Dinkin Duniya kan rikicin Siriya, Stanfan De Mistura da shi ma yake halartar taron.

A tsakiyar watan Satumba da ya gabata ne shugabannin kasashen Rasha da Turkiyya suka cimma yarjejeniyar tsagaita wuta a yankin na Idleb, yanki na karshe dake hannun mayakan dake ikirari da sunan jihadi a arewacin kasar Siriya.

Ana dai fatan taron zai samar da hanyoyin  isar da kayan agaji ga fararen hula cikin gaggawa.

 

 

Tags