Oct 31, 2018 12:04 UTC
  • Amurka ta Baiwa Masu Rikici A Yemen Kwanaki 30 Kan Su Tattauna

Amurka ta bukaci bangarorin dake rikici a Yemen dasu kawo karshen rikicin kasar tare da gindaya masu wa'adin kwanaki talatin na su bude tattaunawa tsakaninsu.

Sakataren harkokin tsaron Amurka James Mattis ne ya bayyana hakan a taron sha'anin tsaro  da ya gudana makon jiya a Bahrain.

Mista Mattis ya bayyana cewa kasashen Saudiyya da Hadaddiyar Daular Larabawa sun ce a shirye suke don shiga tattaunawar.

Shi a nasa bangare ministan harkokin wajen Amurka Mike Pompeo, a jiya Talata ya bukaci kawancen da Saudiyya ke jagoranta a kasar ta Yemen da ya kawo karshen hare hare ta sama da kuma hare haren da su ma 'yan Houtsis ke kaiwa.  

Alkalumman da MDD ta fitar sun nuna cewa mutane kimanin 10,000 ne suka mutu a rikicin kasar ta Yemen.

Tags