Nov 06, 2018 05:25 UTC
  • Kasashen Duniya Na Ci Gaba Da Nuna Adawarsu Da Sake Kakabawa Iran Takunkumi Da Amurka Ta Yi

Kasashe da cibiyoyin kasa da kasa na ci gaba da nuna rashin amincewarsu da sake kakabawa Iran takunkumi da Amurka ta yi, suna masu shan alwashin ci gaba da harkokin kasuwanci da Iran din da kuma riko da yarjejeniyar nukiliyan da aka cimma da kasar.

Kamfanin dillancin labaran Hukumar Gidan Radiyo da Talabijin na Iran ya bayyana cewar kasar Jamus ta bakin kakakin gwamnatin kasar, Steffen Seibert, ta ce tana ci gaba da binciken hanyoyin da za a bi wajen ganin an kiyaye alaka ta kasuwanci da ke tsakaninta da Iran.

Ita ma gwamnatin Birtaniyya ta sanar da cewa sabon takunkumin da Amurkan ta sanya wa Iran ba abin da za a amince da shi ba ne, tana mai sake jaddada aniyarta ta ci gaba da kiyaye yarjejeniyar nukiliya da aka cimma da Iran.

Kasar China ma ta bakin kakakin ma'aikatar harkokin wajen kasar, Hua Chunying, ta bayyana rashin amincewarta da matsayar gwamnatin Amurka na sake kakabawa Iran takunkumi, yana mai kiran da a ci gaba da harkokin kasuwanci da Iran din.

A jiya ne dai sakataren harkokin wajen Amurkan Mike Pompeo da ministan kudin kasar Steven Mnuchin suka sanar da sake dawo da takunkumin a kan Iran budu da kari kan sanar da sunayen mutane da kamfanoni 700 na Iran cikin wadanda aka dankara musu takunkumin.

Tags