Nov 12, 2018 08:03 UTC
  • An Cabke Mutum 2 Da Ake Zargin Kona Motoci Sama da 20 A Faransa

Jami'an 'yan sandar kasar Faransa sun sanar da kame wasu mutum biyu da ake zargin sunada hanu wajen kone motoci sama da 20 a garin Grenoble dake kudu maso gabashin kasar.

Hukumar 'yan sandar kasar Faransa ta sanar da cewa a ranar asabar din da ta gabata wasu mutane sun sanya wuta a kan wasu motoci 21 da manyan motoci guda 4 da gangam a garin Grenoble, inda aka tura jami'an kwana-kwana kimanin 20 domin kashe wutar.

Kafafen yada labaran kasar Faransa sun habarta cewa jim kadan bayan kona motocin, 'yan sanda sun yi shakkun wata mota inda suka bi bayanta sannan suka yi awan gaba da mutanan biyun dake cikinta, inda suka tuhume su da cinna wuta ga motocin.

'Yan sandar kasar Faransan sun yi Allah wadai kan yadda rashin tsaro ke kara wanzuwa a yankunan kudancin kasar musaman ma a garin Marseille.

Ayyukan 'yan bata gari na daga cikin dalilan dake janyo wanzuwar rashin tsaro a garin na Marseille.

Tags