Nov 18, 2018 06:27 UTC
  • Zanga-Zangar Kin Amincewa Da Karin Farashin Makamashi A Faransa Ta Lashe Ran Mutum Guda

Zanga-zangar nuna rashin amincewa da karin farashin makamashi a kasar Faransa ta lashe ran mutum guda tare da jikkata wasu fiye da hamsin na daban.

Dubban daruruwan mutane ne suka fito zanga-zangar nuna rashin amincewa da matakin gwamnatin Faransa na kara farashin makamashi a kasar, inda a safiyar jiya Asabar masu zanga-zangar suka toshe-manyan hanyoyi a birane daban daban ciki har da birnin Paris fadar mulkin kasar lamarin da ya janyo cinkoson ababan hawa a kan tituna.

Rundunar 'yan sandan Faransa ta sanar da cewa: Mutuwar mutum guda a yayin zanga-zangar hatsari ne da ya faru bisa kuskure sakamakon kubcewar sitayarin mota a hannun wani direban mota a lokacin da yayi kicibis da masu zanga-zangar lamarin da ya janyo bankade wata tsohuwa 'yar shekaru kimanin 60 a duniya da ya yi sanadiyyar mutuwarta, sannan zanga-zangar ta rikide zuwa tarzoma da ta yi sanadiyyar jikkata mutane da dama.

Siyasar shugaban Faransa Emmanuel Macron ta gudanar da gyare-gyare a harkar tattalin arzikin kasar ciki har da karin farashin haraji a kan makamashi, tana ci gaba da fuskantar adawa daga al'ummar kasar. 

Tags