Nov 20, 2018 09:19 UTC
  • Amurka Ta Kakaba Wa Wani Dan Kasar Afirka Ta kudu Takunkumi

Baitul-Malin kasar Amurka ne ya sanar da kakawa Vladlen Amtchentsev takunkumi saboda ya keta takunkumin man fetur da Amurka ta sa'a kasar Korea ta Arewa.

An shigar da sunan Vladlen Amtchentsev  ne a jerin sunayen da Amurka take sa wa takunkumi, saboda ya bai wa korewa Ta Arewa shawara akan yadda za ta kaucewa takunkumin da Amurka ta kakaba mata.

A can kasar Singapore ma Amurka ta kakabawwasu kamfanoni biyu takunkumi sai kuma wani mutum guda, dukkaninsu saboda yin mu'amalar kudade da kasar Korea ta Arewa.

Amurkan na ci gaba da kakabawa Korea ta Arewa takunkumi ne duk da kokarin da kasar take yi na ganin an sami sulhu a yankin Korea.

Tags