Nov 22, 2018 07:45 UTC
  • Ana Ci Gaba Da Tashe-tshen Hankula A Kasar Faransa

A kalla 'yan sanda 30 ne su ka jikkata sanadiyyar tashe-tashen hankulan da suke faruwa a kasar Faransa

Kakakin gwamnatin Faransa Benjamin Griveaux ya bayyana cewa ya zuwa yanzu an kame mutane 109 da suke da hannu a tashe-tashen hankula, kuma 'yan sanda 30 sun jikkata

Kakakin gwamnatin ta Faransa ya kuma bayyana cewa; A daren laraba ma an ci gaba da samun tashe-tashen hankula a yankuna daban-daban na kasar da suka hada da birnin Paris, inda aka girke wasu karin 'yan sandan 107

Mutanen Faransa suna nuna kin amincewarsu ne da shirin gwamnatin kasar na kara farashin makamashi. Tun ranar asabar din da ta gabata ne dai al'ummar kasar suka fara gudanar da zanga-zanga akan titunan kasar ta Faransa.

Tags