Nov 24, 2018 05:49 UTC
  • An Gurfanar Da Madugun 'Yan Daban Afirka Ta Tsakiya A Gaban Kotun ICC Da Ke Hague

An gurfanar da tsohon madugun 'yan daban kasar Afirka ta Tsakiya Alfred Yekatom wanda aka fi sani da Rambo a karon farko a gaban alkalan kotun kasa da kasa mai shari'ar manyan laifuffukan yaki da ke birnin Hague, mako guda da mika shi ga kotun da gwamnatin Afirka ta tsakiyan ta yi.

Kafar watsa labaran Africanews ta bayyana cewar a jiya Juma'a ce dai aka gurfanar da Alfred Yekatom a gaban alkalan kotun ta ICC bisa zargin aikata laifuffukan yaki a kasar Afirka ta tsakiyan daga watan Disamban 2013 zuwa Disamban 2014.

Rahotanni sun ce an gudanar da zaman kotun na jiya ne din ne dai don alkalan su tabbatar da wanda ake zargi shi ne da kansa, tantance yaren da wanda ake zargin zai yi amfani da shi yayin shari'ar bugu da kari kan sanar da shi cajin da ake masa.

A ranar 29 ga watan Okotoban da ya wuce ne jami'an tsaron kasar Afirka ta tsakiya suka kama Mr. Yekatom wanda kotun ta ICC take nema saboda zargin tarwatsa musulmin kasar da azabtar da su, sannan kuma suka mika shi ga kotun ta ICC a ranar 17 ga watan Nuwamban nan

Babban alkalin kotun ya sanya ranar 30 ga watan Aprilun shekara mai kamata ta 2019 a matsayin ranar da za a sake gurfanar da shi Mr. Yekatom din a gaban kotun don ci gaba da yi masa shari'a.

 

Tags