Nov 24, 2018 19:19 UTC
  • Faransawa Na Ci Gaba Da Yin Bore Akan Karin Kudin Makamashi

Mazauan tsibirin Reunion na kasar ta Faransa sun fito kan tituna domin yin Zanga-zangar nuna kin amincewa da karin kudin makamashi

Kamfanin dillancin labarun Faransa ya ambato cewa; Mazu zanga-zangar sun datse manyan hanyoyin tsibirin na Reunion, suna masu zargin gwamnati da rashin adalci da kuma nuna wariya akan 'yan kasa.

Wani mai zanga-zangar ya fadawa kamfanin dillancin labarun Faransa cewa; Jin dadi ya kare a tsibirin , dukkanin mazaunansa suna koke.

Ministan harkokin cikin gidan Faransa Christopher Castaner ya tsallake rijiyar da baya bayan da aka kai masa hari da wani abu mai fashewa a garin Angers.

A babban birnin kasar ta Faransa wato Paris masu Zanga-zangar sun yi taho mu gama tare da jami'an tsaro.

 Kawo ya zuwa yanzu mutane biyu sun rasa rayukansu yayin da wasu 650 suka jikkata.

Tags