Dec 01, 2018 05:23 UTC
  • Shugaba Macron Ya Jaddada Wajibcin Gudanar Da Bincike Na Kasa Da Kasa Kan Kashe Khashoggi

Shugaban kasar Faransa, Emmanuel Macron ya bayyana wajibcin gudanar da bincike na kasa da kasa dangane da kisan gillan da aka yi wa Jamal Khashoggi, dan jarida dan kasar Saudiyya mai suka gwamnatin kasar, da aka yi a karamin ofishin jakadancin Saudiyyan da ke birnin Istanbul na kasar Turkiyya.

Kamfanin dillancin labaran Reuters ya ce shugaba Macron din ya bayyana hakan ne a wata ganawa da yayi da Yarima mai jiran gado na Saudiyya a bayan fagen taron shugabannin kasashen kungiyar G20 da aka gudanar a kasar Arjentina inda ya ce kasashen Turai dai suna kan bakansu na a gudanar da bincike na kasa da kasa kan kisan gillan da aka yi wa Khashoggin.

Kafofin watsa labarai sun watsa wani faifan sautin da aka dauka inda Yariman Saudiyya din yake kokarin kwantar wa shugaban Faransan hankali kan batun kashe Khashoggin sai dai shugaba Macron din ya bayyana masa cewa lalle suna cikin damuwa kan batun.

A farko-farkon watan Oktoban da ya gabata ne dai wasu jami'an tsaron da gwamntin Saudiyyan ta tura kasar Turkiyya suka kashe Jamal Khashoggin a karamin ofishin kasar da ke birnin Istanbul lamarin da kafofi da dama suke ganin akwai hannun Yarima mai jiran gadon cikin wannan danyen aikin.

Tags