Dec 02, 2018 17:22 UTC
  • Faransa : Taron Gaggawa Kan Boren Jama'a

Shugaba Emanuel Macron na Faransa ya jagoranci wani taron gaggawa tare da wani bangare na gwamnatinsa a yau Lahadi, domin tattauna halin da kasar ke ciki a daidai lokacin Faransawa ke ci gaba da zanga-zangar adawa da tsadar rayuwa.

Taron dai na zuwa kwana guda bayan gagarimar zanga-zangar da Faransawan suka gudanar a jiya Asabar a sassa daban daban na kasar, wacce kuma ta haddasa barna mai yawa musaman dandalin ''Chant Elysse'' dake a Paris babban birnin kasar.

A yayin taron na yau, Mista Macron dai ya bukaci Firaministansa, Edouard Philippe, da ya tattauna da wakilai da kuma jagororin masu boren « gilets jaunes ko Yellow vests ».

Haka kuma shugaba Macron ya bukaci ministan cikin gida na kasar da ya dauki kwararen matakai na tsaro saboda nan gaba, duba da irin barnar da aka yi a birnin, wanda a cewarsa a abinda za'a zamunta da shi ne ba, don kuwa akwai bata-gari dake fakewa da boren.

Alkalumman baya bayan nan da ma'aikatar cikin gidan Faransa ta fitar, sun nuna cewa mutane 263 ne suka raunana a zanga zangar ciki har da jami'an tsaro 23, a yayin da kuma ake tsare da mutane 378.

Mutane kimanin 136,000 ne suka shiga zanga zangar ta jiya Asabar a duk fadin kasar, sabanin 166,000 da suka shiga boren a ranar 24 ga watan Nuwamba da ya gabata.

Tags