Dec 12, 2018 04:18 UTC
  • Dan Bindiga Ya Hallaka Mutum AKalla 4 A Faransa

Rahotanni daga Faransa na cewa mutane a kalla hudu ne suka mutu a yayin wata musayar wuta a tsakiyar birnin Strasburg da yammacin jiya Talata.

A yanzu haka dai an ayyana shirin ko ta kwana a fadin kasar, biyo lamarin da ya yi sanadin mutuwar mutum uku da raunata wasu 12, da suka hada da guda shida dake cikin mawuyacin hali a cewar ministan cikin gida na kasar Christophe Castaner. 

Bayanai daga kasar sun ce an karfafa kwararen matakai na jami'an tsaro a birnin da iyakokinsa, a yayin da kuma 'yan sanda ke ci gaba da farautar maharbin.

Tuni dai aka tantance maharbin mai shekaru 29, wanda kuma aka bayyana shi a matsayin sanane kasancewar ya taba yin kaso saboda wasu ayyukansa da halaye da suka hada rikici da kuma nacewa kan addini.

A game da hakan dai sashen yaki da ta'addanci na kasar ya ce yana da kwararen hujjoji domin bude bincike kan kisa da yunkurin kisa mai nasaba da kungiyoyin 'yan ta'adda.

Tags