Dec 13, 2018 19:02 UTC
  • An Kashe Yahudawan HKI 2 A Yankin Yamma Da Kogin Jodan

Wani bafalasdine ya harbe yahudawan sahyoniya biyu har lahira kwana guda bayan da yahudawan suka kashe Palasdinawa biyu yan kungiyar Hamas a yankin yamma da kogin Jordan.

Tashar talabijin ta Presstv ta bayyana cewa majayar yahudawan HKI ta bayyana cewa wani Bafalasdine ya kashe yahudawa biyu sannan ya raunata wani guda a yankin Asaf daga arewacin birnin Qudus.

A wani labarin da wata tashar radiyon yahudawan ta watsa ya ce an kashe bafalasdinen a take bayan harin. A cikin wannan halin na tashin hanali sojojin yahudawan sun yi wa garin Ramalla kawanya sannan sun aiko da karin sojoji zuwa yankin. 

Har'ila yau sojojin yahudawan sun kashe wani Bafalasdine a cikin tsohon birnin Qudus bayan sun tuhume shi da dabawa wani bayahude wuka a yau Alhamis.

A wani labarin kuma sojojin yahudawan sun kashe Palasdinawa 2 a yankin yamma da kogin Jordan bayan zarginsa da kai hari kan yahudawa a yankin. Banda haka, a wani labarin kuma, sojojin yahudawan sun kashe bafalasdine guda a birnin Nablus,  Yahudawan sun kashe Ashraf Na’alwa dan shekara 23 a duniya ne bayan zarginsa da laifin kissan yahudawa biyu a cikin watan Octoban da ya gabata a yankin yamma da Kogin Jordan.

Kungiyar Hamsa ta tabbatar da cewa wadanda aka kashe yayan kungiyar ne.

 

Tags

Ra'ayi