"Yan Sandan Kasar Faransa Sun Shiga Cikin Masu Zanga-Zangar Fada Da Tsarin Jari Hujja
Majiyar 'Yan Sandan kasar ta Faransa ta ce; Za a rufe dukkanin ofisoshin 'yan sanda domin nuna rashin amincewa da rashin adalci na gwamnati
"Yan Sandan sun yi zargin cewa da akwai bashin da suke bin gwamnatin kasar na karin ayyukan da su ka yi na sa'o'in miliyan 32. Don haka 'yan sandan sun cewa a yanayi irin wannan ba za su iya dakatar da barazanar ayyukan ta'addanci ba a lokacin bukukuwan sabuwar shekara ta Kirsimeti
Ministan harkokin cikin gidan kasar ta Faransa Christopher Castaner zai gana da wakilan 'yan sandan a yau Talata
Kasar Faransa tana fuskantar Zanga-zanga mafi girma wacce ba a ga irinta ba a cikin shekarun bayan nan wacce aka yi wa lakabi da masu rawayar taguwa.
Masu Zanga-zangar suna fada ne da karin farashin makamashi, da kuma wasu tsare-tsaren tattalin arzikin kasar