Dec 28, 2018 06:42 UTC
  • Masu Neman Sauyin Tsarin Tattalin Arziki A Faransa Zasu Gudanar Da Zanga- Zanga A Gobe

Masu zanga-zangar neman shugaban kasar Faransa ya sauya tsarin tattalin arzikin kasar sun ce zasu fito gobe Asabar don ci gaba da zanga-zanga.

Kamfanin dillancin labaran AFP na kasar ta Faransa ya nakalto kakakin masu zanga-zangar wadanda aka fi saninsu da farmalan ruwan guro Latisha Duval yana fadar haka, ya kuma kara da cewa, indan gwamnatin shugaban Mocron bata biya bukatarsu na sake nazarin tsarinsa na tattalin arziki ba a gobe asabar zasu fito kan tituna a birnin Paris da kuma sauran garuruwan kasar a karo na 7 don nuna rashin ammincewarsu da tsarin.

Wani daga cikin masu zanga -zangar mai suna Benjamin Cauchy ya fadawa AFP cewa a wannan karon dukkanin biranen kasar Faransa zasu fito don nuna rashin amincewarsu da tsarin tattalin arziki na shugaban Mocron mai kuntatawa talakawa. 

 A cikin makonnin da suka gabata rikici tsakanin jami'an tsaro da masu zanga -zanga ya kai ga mutuwat mutane goma da kua raunata daruruwa, da kuma kama wasu. 

Tags