Jan 01, 2019 06:44 UTC
  • Yansanda Dubu 147 Suka Shirya Tsap Don Murkushe Duk Wata Zanga-Zanga A Faransa

Ma'aikatar cikin gida na kasar Faransa ta bada sanarwan cewa ta tanaji jami'an tsaro dubu 147 don tabbatar da zaman lafiya a daren sabuwar shekara ta 2019.

Kamfanin dillancin labaran AFP na kasar Faransa ya nakalto wani bayani wanda ma'aikatar ta fitar yana cewa ta tanaji dakaru dubu 147 don hana duk wani tashin hankali a daren sabuwar shekara a dukkan manya manyan tituna da wuraren taron jama'a a cikin manya-manyan biranen kasar. 

Ma'aikatar cikin gidan ta kara jaddada cewa ba zata lamuncewa wani ya gudanar da zanga-zanga a cikin daren na yau ba, ko kuma lalata gine-gine da kayakin mutane. 

Makonni 7 kenan wasu masu adawa da tsarin jari hujja suke zanga zanga na yin allawadai da tsarin tattalin arziki na shugaban Emmanuel Macron, wanda ya hada da kara haraji na makamashi. 

Sai dai duk tare da cewa gwamnatin ta jnaye harajin da ta karawa makamashi amma wadanan masu zanga zangar wadanda suke sanye da ruwanguron Farmala sun ci gaba da nuna rashin amincewarsu da tsarin tattalin arziki na shugaban. 

Tags