Jan 08, 2019 06:59 UTC
  • Faransa: Ba Sani Ba Sabo Ga Masu Zanga-Zanga Ba Tare Da Izini Ba.

Firai ministan kasar Faransa ya bayyana cewa jami'an tsaron kasar zasu yi dirar mikiya a kan duk wanda ya fito zanga-zanga ba tare da izini a kasar ba.

Kamfanin dillancin labaran Fars na kasar Iran ya nakalto Edouard Philippe yana fadar haka a jiya litinin ya kuma kara da cewa jami'an tsaron kasar a shirye suke su farwa duk wanda yake son tada hankali a kasar.

A karshen shekara da ta gabata dai mutane 10 ne aka tabbatar da cewa sun rasa rayukansu sanadiyyar dirar mikiyan da jami'an tsaron kasar Faransa suka yiwa masu zanga-zangar kin jinin gwamnatin shugaba Emmanuel Macron.

Sannan wasu mutane dubu 8 kuma suka ji rauni ko aka kamasu.

Tun ranar 17 ga watan Nuwamban shekarar da ta gabata ce mutanen kasar Faransa suka fara zanga-zangar yin korafi kan tsadar makamashi da kuma harajin da tsarin tattalin arzikin shugaban Macron ya dorawa mutanen kasar.

Ba'a dade ba zanga-zangar ta zama ta siyasa inda masu nazarin siyasar kasar suka bayyana cewa kimani kashi 3/4 na mutanen kasar faransa basa goyon bayan tsarin tattalin arzikin shugaba Macron

Tags