Jan 10, 2019 12:26 UTC
  • An Zargi Kasar Faransa Da Haddasa Sabon Rikici A Kasar Afrika Ta Tsakiya

Wasu yan siyasa a kasar Afrika ta Tsakiya suna zargin gwamnatin kasar Faransa da kokarin haddasa wata sabuwar fitina a kasar Afrika ta tsakiya.

Radiyo swahili a nan JMI ya nakalto majiyar wasu yan siyasa a kasar Afrika ta tsakiya suna fadar haka. Sun kuma kara da cewa a farkon wannan shekara ne gwamnatin kasar Faransa ta samar da wata sabuwar kungiyar yan tawaye wacce ta belle daga kungiyar Seleka, wacce kuma aka sanya mata suna ""People's Front for the Revival of the Central African Republic" sannan ta taimaka mata ta kwace iko da birnin Bakuma daga kudancin kasar.

Masana harkokin siyasa sun bayyana cewa manufar kafa wannan kungiyar da kuma mamayar birnin Bakuma da ta yi, har'ila yau da kuma korar dukkan ma'aikatan gwamnati daga birnin ya nuna cewa gwamnatin kasar Faransa ta na son  yi amfani da kamfanin hakar Uranium na kasar Areva wacce take hakkar Uranium a birnin don kwasar arzikin kasar. 

Kafin haka shugaban kasar ta Faransa Emmanuel Macron ya gana da tokoransa na kasar Chadi  Idris Debi inda ya bukace shi ya shiga rikicin kasar Afrika ta tsakiya don dawo da zaman lafiya. Mai yuwa samar da wannan kungiyar shi ne manufar shuwagabannin kasashen biyu.

Tags