Jan 12, 2019 16:54 UTC
  • Ana Ci Gaba Da Zanga zanga A Faransa

Rahotanni daga Faransa na cewa dubban masu zanga zanga ne suka sake fitowa yau Asabar domin ci gaba da zanga zangar neman shugaban kasar Emanuel Macron da ya yi murabus.

Zanga zangar dai na zuwa ne duk da shan alwashin da hukumomin Faransa suka yi na hukunta masu tada rikici a boren.

Hukumomin Faransar wadanda keda fargaba akan zanga zangar sun jibge jami'an tsaro da suka hada da 'yan sanda da kuma jandarma 80,000 a fadin kasar, da suka hada da 5,000 a Paris babban birnin kasar.

Wannan dai shi ne karo na tara da masu zanga zangar da ake kira ''gilets Jaunes'' ke fitowa ko wanne mako domin yin zanga zanga kan tsadar rayuwa, da nuna halin-ko-in-kula ga bukatun talakawan kasar.

Wannan lamarain dai ya kasance kalubale mafi muni da gwamnatin Emanuel Macron ke fuskanta tun bayan da dare kan karagar mulkin kasar a cikin shekara 2017. 

Tun a ranar 17 ga watan Nuwamba bara ne masu zanga zangar ke bore kan wasu matakai da suka ce gwamnatin Faransar ta dauka wandanda kuma zasu fi takurawa masu karamin hali.

 

Tags