Jan 14, 2019 03:58 UTC
  • Amurka : Trump Ya Yi Barazanar Wargaza Tattalin Arzikin Turkiyya

Shugaba Donald Trump, na Amurka, ya yi barazanar wargaza tattalin arzikin kasar Turkiyya, muddin ta kai wa Kurdawan Siriya hari, bayan janyewar sojojinta a Siriyar.

Trump wanda ya bayyana hakan a shaffinsa na twitter, ya ce Amurka zata wargaza tattalin arzikinTurkiyya idan ta kaiwa Kurdawa hari, tare kuma da kira ga Kurdawan da kada su takali mahukuntan Ankara.

Shugaban na Amurka, ya kuma yi kira da a samar da wani yanki na ''tudun mun tsira'' mai cikaken tsaro na tsawan kilomita 30, saidai ba tare da yin karin haske ba.

Wannan furicin na Trump, na zuwa ne a daidai lokacinda sakataren harkokin wajen kasarsa, Mike Pompeo ke gudanar da wani ran gadi a yankin na gabas ta tsakiya, domin kwatar wa da kawayen Amurkar hankali, a daidai lokacin da ake fuskanatr takun-tsaka tsakanin Turkiyyar da Amurka kan batun Kurdawa Siriya, da suka dafawa Amurka baya a yaki da kungiyar 'yan ta'adda ta (IS).

Amurka dai na neman kwantar wa da mayakan Kurdawan hankali da kuma tabbatar masu da kariyar Amurkar koda ta janje sojojinta data jibge a Siriya.

A watan Disamba da ya gabata ne Shugaban Donald Trump na Amurka, ya sanar da matakin shirin janye sojojin kasarsa 2,000 daga Siriya, matakin da gwamnatin Ankara dama wasu kasashen yankin irinsu Iran suka ce Allah ya raka-taki gona, kasancewar tun farko ma babban kuskure ne sanya kafar Amurka a yankin gabadaya.

Tags