Jan 18, 2019 06:46 UTC
  • Kama 'Yar Jarida Marzieh Hashimi Ma'aikaciyar Presstv A Amurka

Duk da cewa gwamnatin kasar Amurka takan nuna kanta a matsayin kasa wacce take kan gaba a kokarin kare hakkin fadin albarkacin baki, da kuma na yan jaridu a duniya, amma a aikace ita ce a gaba wajen take hakkin yan jaridu da makamancinsu a duniya.

A irin wannan halin nata ne, a baya-bayan nan ta kama Marziya Hashimi yar jarida mai karanta labarai a tashar talabijin ta turanci da ke nan birnin Tehran watp Presstv, bayan da ta isa tashar jiragen sama na St. Louis, sannan daga baya aka maida ita zuwa birnin Washington. 

Marziya Hashimi dai, ta musulunta ne bayan nasarar Juyin juya halin musulunci a nan Iran, sunanta na asali shi ne "Melanie Franklin" . an haifeta jihar Colerado na kasar ta Amurka kuma tana da digiri a fannin yada labarai kafin ta taho kasar Iran. 

A kasar Iran bayan karatun addini ta shiga aiki da tashar Telebijin ta watsa labarai da harshen turanci ta Presstv na shekaru masu yawa, amma a makon da ya gabata ne ta je kasar Amurka don ganin danji musamman wani dan'uwanta wanda bai da lafiya sai ta fada hannun yansanda FBI na kasar Amurka, wadanda ba tare da gabatar da wani dalili na kamata ba suka kamata, suka sanya mata anko a hannu da kada suka cire mata hijabinta, sannan suka hanata cin abinci halal. Marziya ta sami magana da diyarta wacce take nan Tehran inda ta fada mata halinn da ta ke ciki,.

Wata daya kafin kama Marziya Hashimi, kungiyar "yan rahoto ba iyaka " ta kasa da kasa ta bada sanarwan ta na shekara-shekara inda a cika ta bayyana cewa kasar Amurka ita ce kasa mafi hatsari ga yan jarida a duniya a halin yanzu.

Wani masani harkokin saiyasar Amurka  Bruce Dixon ya fadawa tashar talabijin ta Presstv kan cewa, 'yencin fadin albarkacin baki a Amurka a baki ne kawai, amma a aikace wani abu daban suke aikatawa. Bruce Dixon ya ce gwamnatocin Amurka karkashin Jagorancin Obama da kuma Donal Trump a halin yanzu sun fi azabtar da yan jarida, sannan wani lokaci ma akan gurfanar da su a gaban koto don hukuntasu a kan rahotonni da suka bayan, wadanda basu ji dadinsu ba. 

Don haka kama Marziya Hashimi wani mataki ne wanda baya bisa ka'ida wanda jami'an tsaron Amurka suka dauka, banda haka irin mummunan halin da suke tsare da ita ya sabawa dokokin kari hakkin bil'adama. Sannan bugu da kari, kowa ya san yadda gwamnatin Amurka ta yanzu, karkashin shugabancin Donal Trump yadda ta zama ta nuna wariya, da kuma kiyayya ga musulmi, musamman kuma bakar fata, babu mamaki idan sun aikata haka da ita. Daga karshe muna rokon Allah ya bata hakurin jurewa duk halin da zasu sanyata a ciki ya kuma taimaka a gaggauta sakinta .

 

Tags