Jan 18, 2019 06:47 UTC
  • Jami'a Mai Kula Da Lamuran Harkokin Wajen Tarayyar Turai Ba Zata Halarci Taron Gangami A Kan Iran Ba

Wata majiya ta Tarayyar Turai ta bayyana Federica Mugareni jami'a mai kula da lamuran harkokin waje na tarayyar ba zata halarci taron "gangami a kan Iran" wanda Amurka zata jagoranta a kasar Polanda ba

Kamfanin dillancin labaran IRNA na kasar Iran ya nakalto majiyar ta Tarayyar Turai wacce bata son a bayyana sunanta tana cewa, Mugareni ba ta da wani shiri na halattar wannan taron, banda haka a randa za'a gudanar taron tana da wasu tafiye-tafiye zuwa wasu kasashen daban.

Sakataren harkokin wajen kasar Amurka Mike Pompeo ya bada sanarwan a ranar Jumma'an da ta gabata kan cewa za'a gudanar da taron "gangami a kan Iran " a ranakun 13 da 14 na watan Febreru mai kamawa a birnin Waso na kasar Poland.

Ministan harkokin wajen kasar Iran Mohammad Jawad Zarif a lokacinda yake maida martani a kan wannan makircin na kasar Amurka a shafinsa na Tweeter ya bayyana cewa, gwamnatin kasar Iran tana kara karfi a ko da yauce, sannan kasashen da zata halarci wannan taron sai matacciyar kasa ko ba za su iya sabawa umurnin Amurka ba. 

Tags