Jan 19, 2019 15:06 UTC
  • Faransa : Ana Ci Gaba Da Zanga-zangar Kin Jinin Macron

A Faransa an shiga sama da wata biyu, na boren da wasu 'yan kasar ke yi na kin jinin gwamnatin shugaba Emanulle Macron.

Wannan dai iata ce Asabar ta goma, da masu zanga zangar ke fantsama kan tutuna domin yin allawadai da abunda suka kira kunnen uwar shegu na gwamnatin kasar akan bukatun talakawa.

Zanga zangar ta yau na zuwa ne duk da muhawarar hadin kan al'umma da shugaban kasar ya kaddamar domin kwantar da hankulan jama'a.

Wata daga cikin masu zanga zangar mai suna, Sophie Tissier, ta shaidawa bayyana a wata hira da kamfanin dilancin labaren AFP cewa, '' Macron bai ji, bai kuma gane abunda ke faruwa, muna so mu bude masa ido, akan wahalar da al'umma ke sha''

Bayanai sun nuna cewa fitowar jama'a a zanga-zanga a wannan karo ma, ya nuna kasawar shugaban kasar wajen kwantar wa da jama'a hankali.

Alkalumman da mahukuntan kasar suka fitar sunyi nuni da cewa, a ranar Asabar data gabata, sama da mutane 80,000 ne suka fito zanga zanga, a yayin da aka wannan karo ma aka jibge jami'an tsaron 'yan sanda da jandarma kimanin 80,000.

Tags